Halvardeh ko Halva Shekari

Halvardeh ko Halva Shekari

Halvardeh ko Halva Shekari, na daya daga cikin alawoyin kasar Iran mai matukar amfani ga jikin dan adam, kuma anayin wannan alawan ne daga markadadden ridi. Halvardeh tana da dandano mai zaki kuma anfi ci da bredi a lokacin karin kumallo.

Gidan tsara mulki

Gidan tsara mulki

Wannan gida na tsara tsaran mulki na birnin tabriz yana a wannan yanki mai suna azarbaijan wanda yake na gwamnati ne, wannan ginin tsawon shekaru da dama kusan daga shekarar ali dubu daya da dari tara da shida (1906) yazama wurin na shawar wari da duk wanda ke cikin wannan motsi, tarukan na gudana da tsarin mulki na wannan kasa wato Iran.

Godiya al'adar Iraniyawa

Godiya al'adar Iraniyawa

Jama'ar Iran na godiya da kyakkyawan kauyen Khaneqah wanda yake a yankin lardin Kermanshah, suna godiya ga Allah daya basu albarkar noman rumman.

​Kogin hoda (Pink lake) ya wuce Yanayi

​Kogin hoda (Pink lake) ya wuce Yanayi

Mun saba da ganin ruwa a shudi (blue) ko watakila kore-kore (greenish). A nan tafki ne da yazo da yanayi na daban na ruwan hoda. Tafkin Lipar Lake (wanda aka sani da ruwan hoda pink lake) ya samo asali saboda wani abu mai tsabta wanda ke dauke da daruruwan halittun ruwa na planktons a wannan yankin.

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall)

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall)

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall) Magudanar Ruwan Takht-e Soleyman, wanda aka sani da Ab-e Malakh (grasshopper’s water) yana daya daga cikin wurare masu ban-mamaki da aka sani sukai suna sosai a Isfahan, Iran. Ruwan da ke gudana daga Takht-e Soleyman ya ƙunshi wasu sinadirai da suke aiki a matsayin magungunan ƙwari a cikin gonakin yankin.

Lambun Golshan, Tabas.

South Khorasan

Lambun Golshan, ana danganta shi da lokacin daula Zand zuwa daular Qajar kuma lambun yana garin Tabas. An yi wa wannan wuri rajista ne a matsayin daya daga cikin kayan tarihi na kasa a ranar 20 ga watan Dey shekara ta 1355, mai lambar rajista 1310. Wannan lambun shakatawa yana daya daga cikin muhimman lambunan Iraniyawa. Mir Hassan Khan na uku ne da ya fito daga zuriyar Khan ya gina wannan lambu na Golshan wadanda Sarki Nadir Shah ya mallakawa mulkin Tabas. Lambun Golshan na daya daga cikin lambuna masu gangara, kuma yana da babban rami da ruwa ke bubbugowa a ciki a tsakiyarsa, sannan kuma Kwasakwasai na wanka a cikinsa. Akwai kuma shuke-shuke iri-iri wadanna suka dace da kowane yanayi. An kawata wurin da bishiyoyin Kwakwa, nau’o’in bishiyoyin lemu, Inabi da Fulawowin ado kala-kala, sun mayar da wannan lambun a matsayin daya daga cikin fitattun lambuna masu gwanin sha’awa a kasar baki daya. Har ila yau wannan lambu yana samun yawan ziyarar masu yawon bude ido a lokacin hutun sabuwar shekara da matafiya da suke ya da zango musamman lokacin hutun sabuwar shekarar.

6
1
2
5
3
4
8
9
12
16
23
14
25
utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸