Gawurtaccen Dutsen Pardis, da ke kusa da Tekun Gulf a kudancin Iran

Dutsen Pardis yana cikin lardin Boushehr, lardin Iran da yake mafi kusa da layin ‘Equator’ na duniya. An kira shi Pouz wato ‘snout’ da turanci, saboda kamnceceniyarsa da siffar bakin dabbobi.

Jama'ar yankin kuwa na kiran dutsen da sunan yankin da yake, wato “Jam”. Wasu daga cikin ƙauyawan sun yi imanin cewa dutsen yana da maganadisun laso motoci daga nisan kamar mita 100.

Shekaru da suka wuce, wani Ba-Iraniyen mai bincike, masanin ilimin Tarihin Karkashin-kasa (Archeologist) ya gano cewa dutsen shine mafi kusa da rana a duniya.

Bugu da ƙari kuma, yankin yana da Dabinai da ake iya amfani da su ga masu ciwon Suga (Diabetes) da kuma ‘ya’yan itatuwa masu magunguna da dama.

Matafiya ka iya hangen Dutsen Pardis akan hanyar su ta zuwa Firouzabad daga Bandar-Kangan a kudancin Iran.

Province Attractions
pardis