Madatsar Ruwa Ta Amir Kabir.

Idan kana son ganinmadatsar ruwan Amir Kabir, wadda aka gina akan tekun Karaj, to sai ka kama hanyar da ta tashi daga Karaj zuwa Chalus, don ka kashe kwarkwatar ido daga kyawun daya daga cikin madatsun ruwa mafi girma a Iran.Madatsar ruwa ce wacce ta keakan kwari mai zurfi, wacce kuma ruwan dadi ya ke kwararowa cikinta daga kan duwatsu masu tsawo. Wannan madatsar ruwan ce ta ke bai wa birnin Karaj da kuma babban birni( Tehran ) ruwa, daga arewacinta zuwa kudancinta.

An kammala madatsar ruwan ne a shekarar 1957 miladiyya akan tekun na Karaj, an kuma bude ta a 1960. Tsawonsa a sama ya kai mita 180, sai kuma a kwance ya kai mita 390. An kuma ba shi sunan tsohon pira ministan Iran ne a zamanin daular Qajar wanda shi ne Amir Kabir.

Akan hanyar tafiya zuwa arewacin Iran, duwatun al-Burz, za su rika yi maka rakiya har ka isa birnin Mazandaran. A cikin wadannan jerin duwatsun masu tsawo, dutsen da ya fi girma shi ne Damavand, da ya kai mita 5610. Kololuwarsa kuwa ita ce mafi tsawo a duniya. Fadinsa ya kai kilo mita 50, yana cike da kankara a kowane yanayi da hakan ya sa ya ke da idanun ruwan dadi.

Bayan tafiya akan hanyar cikin hanzari, za a isa hanyar karkashin kasa wacce ta ke raba iyakar yankin Karaj da gundumar Mazandaran. Tana da girman gaske, ana kuma kiranta da Kanduwan.

Abin mamaki shi ne da zarar ka fice daga cikin wannanramin, za ka ji cewa hayani ya sauya, za kuma ka ji banbanci a tsakanin yankunan biyu. Za kafara ganin giza-gizai a sararin samaniya, kuma darajar zafi ta ragu sosai idan aka kwatanta da yankin Karaj ko Tehran.

Ga wasu daga cikin hotunanwannan madatsar ruwan.

Province Attractions
karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj karaj