Koren tsibirin Khaneqah.

Khaneqah kyauye ne a tsakiyar gundumar birnin Paveh, a lardin Kermanshah na kasar Iran.

Kauyen nada yanayin bazara da rani; da kuma yanayin sanyi lokacin hunturu.

Mutanen kyauyen suna samun kudin shiga ta hanyar noma, kiwon dabbobi, aikin hannu da aikin lambu.

Gidajen kyauyen suna tsara sune ta yadda rufin gidan wani shine farfajiyar makwabcinsa.

Yanayin shiga garin an kayatashi da itatuwa a bakin shiga garin yadda zasu samu jin dadi da iska maikyau.

Saboda karancin yanayin garin, da jerin tsarin gidajensu, da gidajen al'adunsu, da tsarin yadda kasar garin take da yadda suke zaune tsintsiya madaurinki daya, garin Khaneqah ya zama wuri mai kyawawan yanayi ga masu yawon bude ido.

Province Attractions
1