Iran:Kasuwar Baje Kolin Kayakin Kirar Cikin Gida A Shiraz Zai Kashe Tasirin Takunkuman Tattalin Arziki

Kasuwar baje koli na farko na kayakin
kamfanonin cikin gida na kasar Iran a birnin Shiraz wani babban mataki ne na
kawo karshen tasirin da takunkuman tattalin arzikin kasashen yamma suka yi a
cikin tattalin arziki da kuma rayuwar mutanen kasar Iran.
Kamfanin
dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kamfanonin cikin gida sun
kera bangarori daban-daban na ingijunan da kayakin da ake bukata a cikin gida
40,000 a cikin yanayi na matsin lambar tattalin arziki wanda kasashen yamma
suka dorawa kasar Iran.
Labarin
ya kara da cewa kasuwar baje kolin kayakin daban-daban na Shiraz a lardin Fars
dai ya na baje kolin kayakin da aka kerasu don bukatar kamfanonin sarrafa
sinadaran man fetur, wato Petrochemicals, man fetur da iskar gasa, kamfanonin
sarrafa abinci, da kayakin noma, kamfanonin magunguna, sararin samaniya da
jiragen sama da sauransu.
Kasuwar
baje kolin dai na tsawon kwanaki 4 ne wato daga ranar 21-24 ga watan Yuni da
muke ciki.
Mafi
muhimmanci daga cikin kayakin da kamfanonin cikin gida suka kera ko suka samar
a cikin gida sun hada da “Gas Deodorizer” wanda yake ciriwa ko sanya kanshi iskar
gasa, wanda ake shigo da shi daga kasar Faransa kafin takunkuman tattatalin
arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar.
Har’ila
yau a halin yanzu ana samarda tsarin “relay Box” na injina wadanda suka hada da
na motocin hawa ko wasu injunan daga cikin gida wanda kafin haka kasashen kadan
ne a duniya suke iya sama da shi.