Ana Bata-Kashi A Tsakanin Sojonin HKI Da Palasdinawa “ Yan Gwagarmaya A Jenin

Rahotannin da suke fitowa daka garin Jenin sun ambaci cewa sojojin HKI sun kai hari a kan wani gida dake cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin, da zummar kama wasu ‘yan gwgawarmaya.
Shaidun ganin ido sun ce tun da safiyar
yau ne sojojin mamayar na HKI suka killace gidan, inda su ka fara jefa wasu
abubuwa masu fashewa da kuma bude wuta.
Palasdinawa 4 ne aka tabbatar da cewa
sun jikkata sanadiyyar harin na ‘yan sahayoniya, tare da lalata wani sashe na
gidan da Mahmud dub’i yake ciki.
Wasu kafafen watsa labarun ‘yan
sahayoniya sun ce daya daga cikin sojojinsu na mamaya ya jikkata.
A gefe daya, a yau Juma’an ne ake yin
jana’izar ‘yar rahoton tashar talabijin din aljazira ta Kasar Katar, Shirin Abu
Akilah, wacce sojojin mamaya su ka kashe ta a lokacin da take aikewa da rahoto
daga Jenin.
Kasashe da kungiyoyi da dama sun yi tir
da aikin ta’addancin na ‘yan sahayoniya,tare da yin kira da a hukunta masu
hannu a ciki.