Al’ummar Kasar Sudan Suna Ci Gaba Da Zanga-zanagr Kria Ga Sojoji Da Su Sauka Daga Kan Mulki

2022-05-13 14:51:16
Al’ummar Kasar Sudan Suna Ci Gaba Da Zanga-zanagr Kria Ga Sojoji Da Su Sauka Daga Kan Mulki

A jiya Alhamis 12 ga watan nan an Mayu, al’ummar ta Sudan sun sake komawa kan titunan birnin Khartum, inda suke kira ga sojojin HKI da su fita sha’anin mulki su koma barikokinsu.

Masu Zanga-zangar sun yi cincirindo a kusa da fadar shugaban kasa a binin Khartum da shi ne gangami mafi girma tun bayan karewar wata Ramadan.

Wani daga cikin masu gangamin Abdulmalik Ibrahim ya shaidawa kafar watsa labaru ta Afirca News cewa; Abinda kawai muke so, shi ne majalisar soja mai mulki ta sauka daga kan kujerar mulki ta mikawa fararen hula, saboda a ceto da kasar ta Sudan.”

Ibrahim ya kuma ce; Matukar babu ‘yanci ko adalci, to ba za a sami zaman lafiya ba a kasar.

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne dai sojojin kasar su ke rike da akalar mulki su ka kori dukkanin fararen hular da suke cikinsu, domin zama su kadai ne ke rike dukkanin madafun iko.

Tun a 2019 ne dai kasar ta Sudan take fuskantar zanga-zanga wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Umar Hassan al-Bashir.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!