An Kai Harin Ta’addanci A Karon Farko A Kasar Togo Wanda Ya Kashe Sojoji Da Dama

2022-05-13 14:49:44
An Kai Harin  Ta’addanci A Karon Farko A Kasar Togo Wanda Ya Kashe Sojoji Da Dama

Majiyar gwamnatin kasar ta Togo ta ambaci cewa; A kalla sojojin kasar 8 ne aka kashe, tare kuma da jikkata wasu 13 a wani harin ta’addanci irinsa na farko da aka kai a kasar.

Sanarwar ta ce wasu mutane da ba a kai ga tantance da ko su wanene ba, sun kai hari akan sojoji da su ke a yankin Kpinkankandi da misalign karfe 3;00 NS.

Wani babban jami’in soja ya sanar da cewa; Maharin sun je ne akan Babura 60,kuma sun yi musayar wuta da sojoji na tsawon sa’o’i 2.

Sanarwar gwamnatin da aka karanta a kafafen watsa labarun kasar ta ci gaba da cewa; sojojin da aka kai wa harin suna a yankin ne domin hana masu ikirarin jihadi yin kutse daga kasar Burkina Faso.

Gwamnatin kasar ta Togo ta yi tir da harin ta’addancin, kuma za ta yi duk abinda za ta yi domin gano maharan.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!