Wani Dan Siyasa A Kasar Denmark Ya Sake Kona Al’kur’ani Mai Girma

2022-05-13 14:47:54
Wani Dan Siyasa A  Kasar Denmark Ya Sake Kona Al’kur’ani Mai Girma

Dan siyasar kasar ta Denmark mai wuce gona da iri, Rasmus Paludan ya je yankunan Fropnd da Boras, da mafi yawancin mazaunansu musulmi ne inda ya kona al’kur’ani mai girma domin tsonaka.

Jami’an tsaron kasar ta Danmark da dama ne su ka yi wa dan siyasar rakiya domin ba shi kariya daga musulmin da lamarin ya fusata su.

Tun a 2017 ne dai wannan dan siyasar kasar ta Danmark mai wuce gona da iri, yake yawo a tsakanin garuruwa da unguwannin da musulmi suke zaune inda yake kona alkur’ani mai girma domin tsokana.

A cikin watan Ramadan da ya shude, Rasmus Paludan ya yi irin wannan tsokanar a kusa da masallatan musulmi wanda ya jawo mayar da martani.

Tashe-tashen hankalin da kasar ta fuskanta a lokacin ya yi sandarin kona motocin ‘yan sanda 20 da kuma jikkata wasu 26 daga cikinsu, sai kuma wasu masu zanga-zanga 14.

Gwamnatin Iran ta kira yi kasar Danmarka da ta kawo karshen wannan irin tsokanar da ake yi wa al’ummar musulmi da hana hakan faruwa.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!