Kasashen Ghana, Ruwanda Da Senigal Za Su Kafa Masana’antar Samar Da Allurar Rigakafin Covid -19

2022-01-26 14:47:55
Kasashen Ghana, Ruwanda Da Senigal Za Su Kafa Masana’antar Samar Da Allurar Rigakafin Covid -19

Nana Akufo Addo shugaban kasar Ghana shi ne ya bayyana hakan inda ya kar da cewa kasar Ghana ta kama hanyar kafa masana’antar samar da Allurar rigakafin cutar Covid -19,

Ya ce A ranar 16 ga watan Fabarerun shekarar da muke ciki ne shugaban kasar Senigal Macky Sal da na ruwanda Pail Kagame zasu yi bincike kan kayyakin kere-kere da ake abukata wajen samar da Allurar a kasar Jamus . kuma zamu aiwatar da wani gagarumin aiki tsakaninmu da kawayen mu guda biyu, kuma daga karshe a kafa shi a kasar Ghana.

Yakara da cewa kamfanin Biotech na kasar Jamus dake aiki da kamfanin Pfizer ya amince ya sanya hannun jari kuma ya sha Alwashin taimawa wajen ganin an gina babbar cibiyar ta zamani dn samar da wasu allurar rigakafin cutatttuka kamar Malerya tarin Fuka a kasar Ghana.

Daga karshe ya nuna cewa gwamnatins za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin ta kare Alummar kasa daga duka waa Annobar cuta za ta bullo.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!