MDD Na Bukatar Dala Miliyan 39 Domin Taimakawa Yan Gudun Hijiran Kasar Siriya

2022-01-26 14:45:50
MDD Na Bukatar Dala Miliyan 39 Domin Taimakawa Yan Gudun Hijiran Kasar Siriya

Babban jami’I a hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya Mark Katz ya fadi cewa Akwai bukatar kudi da yawansu ya kai dala miliyan 39 domin taimakwa yan gudun hijirar kasar siriya 250,000 dake zaune a sansanin yan gudun hijira dake areaway maso gabashin kasar.

Gwamnati da Alummar kasar Siriya sun fafata da kungiyar Ta’adda ta ISIS da sauran kungiyoyin ta’adda a kasar na tsawon shakara 10, amma yan zu an samu zaman lafiya da daidaito da kuma kyautatuwar alaka da sauran kasashen yanki, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki na kasa da kasa su bada kulawa ta musamman game da halin da kasar ke ciki. Wajen dake mata takunkumi da sake gina kasar da dawo day an gudun hijira.

Tsananin dussar kanakara dake zuba da ruwan sama kamar dab akin kwarya na shafar yan gudun hijiran kasar sama da 250,000 dake rayuwa a sansani a arewa masu gabashin kasar

Daga karshe Mark Katz ya fadi cewa duk da tsagaita wutan da aka samu amma har yanzu ana kai hare-hare da kuma kai hari ta sama a Arewa maso gabashin kasar

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!