Kungiyar Transparency International Ta Ce Najeriya Ce Ƙasa Ta Biyu Da Aka Fi Cin Hanci Da Rashawa

2022-01-26 14:43:31
Kungiyar Transparency International Ta Ce Najeriya Ce Ƙasa Ta Biyu Da Aka Fi Cin Hanci Da Rashawa

A wani rahoto da Kungiyar Transparency International ta fitar ya nuna ceewa Najeriya ce ƙasa ta biyu cikin ƙasashen da aka fi tafka laifukan cin hanci da rashawa a yammacin Afirka a shekara ta 2020, a cewar.

Yace rashawar da ake tafkawa a ƙasar ya karu kamar yadda rahotanta ke nunawa cikin shekaru biyu.

Najeriya dai na bin Guinea Bissau wacce ita ce ta ɗaya a ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yankin kudu da hamadar saharar Afirka.

Rahoton wanda aka fitar tare da hadin-gwiwar kungiyar da ke fafutukar inganta harkokin majalisun dokoki ta CISLAC ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu koma-baya dangane da yadda al`ummar kasar ke kallon yakin da take yi da cin hanci da rashawa.

Rahoton ya kuma nuna yadda annobar korona ya bankado irin wadanan rashawar da gibin da ake dashi a fanin lafiya da yada aka rinƙa handame kuɗaɗen tallafin gaggawa.

Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya ya ce "Cin hanci da rashawa a harkar tsaro ya ja har aka yi zanga-zangar EndSars.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!