Nijar : An Dawo Da Dokar Hana Amfani Da Babura A Jihar Tillaberi

2021-10-13 14:37:29
Nijar : An Dawo Da Dokar Hana Amfani Da Babura A Jihar Tillaberi

Hukumomi a jihar Tillaberi daye yammacin jamhuriyar Nijar, sun sanar da dawo da dokar hana amfani da babura a wasu sassan jihar dake a yankin nan na iyakoki guda uku da hada Mali, Nijar da Burkina faso mai fama da matsalolin tsaro.

Shafin yada labarai na intanet Actuniger, ya nakalto cewa an dauki matakin ne bisa bukatar wasu mazauna yankunan ga gwamnatin jihar da ta kasar, saboda fargaba game da hare haren ‘yan bindiga a yankin, duk da dan sukunin da aka samu a baya bayan nan game da matsalolin na rashin tsaro.

Dokar wacce ta fara aiki a wannan Laraba, ta shafi lardunan Say, Torodu, Gothèy, Téra, Bankilaré, Ayerou da Tillabéri da kuma yankunan karkara na Dessa da Anzourou.

An amince daukar matakin ne yayin taron majalisar koli ta tsaron kasar da shugaban kasar ya jagoranta a jiya.

A ranar 1 ga watan Agusta da ya gabata gwammanti ta dage dokar hana amfani da babura a jihar ta Tillabery, bayan share shekaru hudu a karkashin dokar saboda dalillai na tsaro.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!