​Iran Da Azerbaijan Sun Jaddada Cewa Alakarsu Ta Zumunci Ce Da Kuma Kawance

2021-10-13 13:12:36
​Iran Da Azerbaijan Sun Jaddada Cewa Alakarsu Ta Zumunci Ce Da Kuma Kawance

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian da ministan harkokin wajen Azerbaijan Jehon Bayramov sun tattauna ta wayar tarho kan sabbin abubuwan da ke faruwa a dangantakar kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada bukatar mutunta juna, inda ya kara da cewa Tehran da Baku suna da dadaddiyar dangantaka a tsakaninsu.

Ya jaddada cewa: dole ne kasashen biyu su kawar da duk wani rashin fahimtar juna a dangantakar su, kuma yana da kyau su ci gaba da alakar su ta hanyar da ta dace ba tare da wani bata lokaci ba.

Yayin da yake ishara da zurfin alakar da ke tsakanin kasashen biyu, ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa, Tehran da Baku suna da abokan gaba kuma bai kamata bangarorin biyu su ba abokan gaba damar kawo cikas ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba, kuma ya kamata a warware damuwarsu ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

Shi ma a nasa bangaren Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Azerbaijan Jihon Bayramov, ya bayyana alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin kawance, inda ya kara da cewa alakar da ke tsakanin kasashen da ke kawance ita ce ked a fifiko ga Jamhuriyar Azerbaijan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!