​Rockland: Babu Abin Da Ya Rage Ga Amurka Sai Ta Yi Mu'amala Da Taliban

2021-09-14 14:42:41
​Rockland: Babu Abin Da Ya Rage Ga Amurka Sai Ta Yi Mu'amala Da Taliban

Masanin harkokin siyasar kasa da kasa a Amurka ya ce babu abin da ya rage ga gwamnatin kasar illa ta yi mu'amala da Taliban.

A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran iqna, Farfesa Michael Aaron Rockland malamin jami'a kuma masanin harkokin siyasar kasa da kasa a Amurka ya ce, babu abin da ya rage ga gwamnatin kasar illa ta yi mu'amala da Taliban.

Michael Aaron Rockland wanda farfesa ne a jami'ar Rutgers ya bayyana cewa, dole ne gwamnatin Amurka ta dauki matakan da suka dace dangane da kasar Afghanistan tun kafin sauran mutuncin da ya rage mata ya karasa zubewa.

Ya ce, tun farko Amurka ta tabka babban kure yadda ta shiga kasar Afghanistan da sunan dawo da doka da oda da kuma murkushe Taliban, domin kuwa babu ko daya daga ciki da Amurka ta iya yi a cikin shekaru ashirin da ta kwashe tana mamaye ad kasar.

bayan janyewarta a cikin makonnin da suka gabata, ya tabbata cewa Amurka ba ta murkushe Taliban ba, ta ma kara karfi nea cikin wadannan shekaru ashirin, kamar yadda kuma Amurka ba ta iya kafa gwamnatin kasar yadda za ta iya tsayuwa da kanta ba.

Farfesa Rockland ya ce, a halin yanzu tun da Taliban ta kwace iko da Afghanistan, domin kaucewa wata musibar, da kuma jefa al'ummar kasar cikin wani mawuyacin halin da ba a san karshensa ba, ya zama dole a kan gwamnatin Amurka ta yi mu'amala da Taliban.

Baya ga haka kuma ya kara da cewa, ta hanyar yin mu'amala da kungiyar, za a iya samun hanyoyi na taimaka ma al'ummar kasar, kuma hakan zai kara sanya Taliban ta zama tana samun canji a tunaninta kan yadda take kallon duniya da siyasarta.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!