MDD, Ta Samu $ Biliyan Guda Domin Tallafawa Afghanistan

2021-09-14 10:03:40
MDD, Ta Samu $ Biliyan Guda Domin Tallafawa Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ta samu sama da Dala Biliyan guda na tallafi domin agazawa al’ummar Afghanistan.

Tallafin ya samu ne bayan taron kasa da kasa da aka gudanar ranar Litini a Geneva domin samar wa da kasar ta Afghanistan tallafi.

Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya yi fatan tallafin zai taimaka wajen ayyukan kare hakkin dan adam a wannan kasa ta Afghanistan.

Kimanin ‘yan Afghanistan miliyan 11 ne ke bukatar tallafin jin kai a cewar MDD.

Mista Guteress, ya bukaci da a tattauna da kungiyar Taliban dake mulki a kasar, saboda a cewarsa ba yadda za’a shayo kan halin da ake ciki a kasar ba tare da damawa da ‘yan Taliban ba.

‘’Ya kuma babu wata riga ga kakaba wa kungiyar Taliban takunkumi’’.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!