Iran Ta Yi Tir Da Harin Ta’addancin Da Ya Lakume Rayuka A Iraki

2021-07-21 10:30:46
Iran Ta Yi Tir Da Harin Ta’addancin Da Ya Lakume Rayuka A Iraki

Iran ta yi tir da Allahwadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a anguwar Sadr City dake Bagadaza babban birnin kasar Iraki.

Akalla mutane 35 ne aka rawaito sun rasa rayukansu, kana wasu sama da 60 suka jikkata a harin da aka kai kan wata kasuwa a daidai lokacin da jama’a ke hada hadar a jajibirin babbar sallah.

Da yake mika ta’aziyar gwamnatin Iran, ga al’ummar kasar ta Iraki, Saeed Khatibzadeh, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, ya ce Iran a shirye take domin karfafa alaka da Iraki wajen yaki da ta’addanci.

Kungiyar Da’esh ce dai ta dauki alhakin kai harin na ranar Litini.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!