Al’amura Sun Fara Daidaituwa A Afrika Ta Kudu

2021-07-21 10:29:30
  Al’amura Sun Fara Daidaituwa A Afrika Ta Kudu

Mukaddashin ministan dake kula da fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Khumbudzo Ntshavheni, ta bayyana cewa, al’amura sun fara dawowa kamar yadda suke, ba tare da samun rahoton wani rikici ba, cikin kwana 1 da ya gabata.

Khumbudzo Ntshavheni, ta bayyana haka ne yayin da take jawabi ga manema labarai game da yanayin da zanga-zangar kasar ke ciki sanadiyyar jefa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma da aka yi a gidan yari.

Ta ce wasu daga cikin manyan shaguna da aka rufe bayan fara rikicin sun bude yanzu, yayin da ayyuka suka kankama a tashoshin jiragen ruwa na Durban da Richards, inda manyan motoci ke zirga-zirga a fadin kasar suna jigilar muhimman kayayyaki.

Akwai kuma jami’an tsaro a dukkan muhimman wurare.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!