Sara Gamal Ta Kafa Tarihi Na Farko A Alkalancin Wasannin Olympics

2021-07-21 10:24:34
Sara Gamal Ta Kafa Tarihi Na Farko A Alkalancin Wasannin Olympics

A rahoton da jaridar Leadership ta bayar, Gamal za ta kasance mace Musulma mai saka hijabi ta farko mai alkalancin wasan kwallon kwando a gasar wasan Olympics sanna ba haka kadai ba, ita kanta tawagar wasan kwallon kwandon da take yi wa alkalancin, shiga gasarta zai kasance na biyu a birnin Tokyo cikin wannan watan na Yuli.

Ana daukar wasan kwallon kwando na 3d3 a matsayin wanda aka fi bugawa a cikin wasannin duniya, wanda ya bunkasa zuwa wasan da akan buga a fadin duniya a lambu da wuraren shakatawa da ake fi sani da Streetball, da Blacktop or Playground Ball.

Sai dai duk da haka an kididdige cewa kasashe 182 da mutane fiye da 430,000 a fadin duniya ne ke buga wasan kwallon kwando na 3d3 hakan yana nufin cewa babu mutane da dama a duniya da suke buga wannan wasan.

Sara kuma za ta kasance Balarabiya ta farko kuma mace ‘yar Afirka da ta jagoranci tawagar wasan kwallon kwando a gasar Olympics kuma a kwanakin baya Sara ta ce addininta ya yi tasiri a aikinta na alkalancin wasa.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!