​Iran: Shugaba Rauhani Ya Isar Da Sakon Murnar Salla Ga Shugabannin Kasashen Musulmi

2021-07-21 09:45:10
​Iran: Shugaba Rauhani Ya Isar Da Sakon Murnar Salla Ga Shugabannin Kasashen Musulmi

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya isar da sakon taya murnar idin sallar layya ga shugabannin kasashen musulmi.

A cikin sakon nasa wanda ya aike wa shugabanni daban-daban na kasashen musulmi, shugaba Rauhani ya bayyana wannan lokaci na idin sallar layya da cewa, lokaci mai matukar muhimmanci ga dukkanin al’ummar musulmi.

Ya ce lokaci na gudanar da ibadar aikin hajji, wadda take daya daga cikin manyan rukunai na addinin muslunci, ibadar da ke hada dukkanin musulmi daga ko’ina cikin fadin duniya domin tabbatar da Kalmar tauhidi da yin aiki da umarnin Allah.

Shugaba Rauhani ya bayyana cewa, har kullum musulmi suna da bukatuwa zuwa ga karfafa alakarsu da kuma kaunar juna, da yin aiki tare a dukkanin bangarori domin ci gabansu, da kuma fuskantar kalu bale da ke a gabansu a mataki na duniya.

Daga karshe ya yi fatan alhairi ga daukacin musulmi na duniya, tare da fatan samun ci gaba da zaman lafiya a dukkanin kasashen musulmi, da bunkasar arziki, da kuma fatan ganin karshen annobar korona wadda ta addabi al’ummomin duniya baki daya.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!