Za’a Koma Bakin Tattaunawar Vienna A Mako Mai Zuwa

2021-06-10 14:30:41
Za’a Koma Bakin Tattaunawar Vienna A Mako Mai Zuwa

Shugaban tawagar Iran a tattaunawar Vienna ta yunkurin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, Abbas Araghtchi, ya sanar da cewa za’a koma bakin tattaunawar a makon gobe.

Abbas Araghtchi, wanda shi ne karamin ministan harkokin wajen Iran, ya ce tattaunawar da aka shafe tsawon makonni anayi, ana nan ana duba yadda bangarorin zasu dawo mutunta yarjejeniyar.

Ya ce a makon mai zuwa zamu shiga wani zagayen tattaunawa, kuma muna fatan ci gaba kan batutuwa da dama, saidai ya yi sauri a ce ko zagayen tattaunawar dake tafe shi ne na karshe.

Tattaunawar da ake saran komawa a makon gobe ita ce karo na shida.

Batun dagewa Iran takunkumai da kuma dawowar Amurka a cikin jarjejeniyar su ne suka mamaye ajadar tattaunawar.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!