ECOWAS Na Son Ganin Bayan Ayyukan Ta’addanci

2021-06-10 14:24:05
ECOWAS Na Son Ganin Bayan Ayyukan Ta’addanci

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana kudirinta na ganin ta cimma nasara a yaki da ayyukan ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.

Shugaban kungiyar ECOWAS mai ci, kana shugaban kasar Ghana Nana Akufi-Addo, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Ghana ta fitar, inda cikinta ya ce, wajibi ne yaki da ta’addanci ya kasance na kowa da kowa.

A don haka, ya zama wajibi ga kungiyar ta hada kai tare da taimakawa kasashe, kamar Burkina Faso, da Nijar, da Mali, wadanda ke kan gaba a yaki da ayyukan ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, ta yadda za su kai ga samun nasara.

Akufo Addo ya bayyana haka ne, yayin ziyarar yini daya da ya kai Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, don jajantawa takwaransa na kasar, Roch Marc Christian Kabore, bayan kisan sama da fararen hula 100 a baya-bayan da ake zargin wasu ‘yan ta’adda da aikatawa.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!