Iran Ta Lallasa Amurka A Wasan Kwallon Raga Na La Liga 2021

2021-06-10 14:22:08
Iran Ta Lallasa Amurka A Wasan Kwallon Raga Na La Liga 2021

Tawagar kwallon raga ta Iran, ta samu nasara ta biyar a gasar la liga ta kwallon raga ta 2021 bayan data lallasa takwararta ta Amurka.

‘Yan wasan na Iran, na volley-ball, sun doke na Amurka ne da ci 3-0, a wasan da suka buka da yammacin jiya Laraba.

Wannan nasarar da ‘yan wasan na kwallon raga na Iran, suka samu, it ace ta biyar a gasar ta 2021, inda suke da maki 15 a cikin wassani bakwai da suka buga.

Wannan ya sanya Iran, ta daga da gurbi guda, inda take a matsayi na biyar a ci gaba da gasar.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!