​Abdollahian: Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Yunkuri Da Zai Kawo Karshen Yaki A Kan Yemen

2021-06-10 10:33:58
​Abdollahian: Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Yunkuri Da Zai Kawo Karshen  Yaki A Kan Yemen

Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan duk wani mataki wanda zai taimaka wajen kawo karshen kisan kiyashi a kan al’ummar kasar Yemen.

Amir Abdollahian ya bayyana hakan ne a yammacin jiya Laraba, a lokacin da yake ganawa da manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Yemen Martin Griffiths a birnin Tehran.

Ya ce ya zama wajibi kan kasar Saudiyya ta kawo karshen yakin da take kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen, domin kuwa ta hanyar wannan yakin ba ta iya cimma abin da take bukata ba na shimfida ikonta a kan kasar, maimakon haka ta bar al’ummar kasar Yemen su zaba ma kansu mafita ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna a tsakaninsu.

Ya kara da cewa, tun da al’ummar kasar Yemen sun nuna cewa ba za su yarda a mulke su ba tare da son ransu ba, to yin amfani da jiragen yaki da kashe dubban fararen hula mata da kananan yara, da rusa masallatai da cibiyoyin kasuwanci da killace kasar ta sama da kasa da ta ruwa, ta jefa al’ummar kasar cikin matsananciyar yunwa, ba zai iya baiwa gwamnatin Saudiyya damar cimma wannan buri nata ba.

Shi ma a nasa bangaren manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Yemen Martin Griffiths ya jinjina wa kasar ta Iran, kana bin da ya kira kokarin da take yi domin ganin an kawo karshen yakin kasar Yemen ta hanyoyi na diflomasiyya da komawa kan teburin tattaunawa tsakanin ‘yan kasar.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!