Firai Ministan Kasar Ivory Coast Ya Ce Ya Sami Lafiya Bayan Dawowarsa Daga Kasar Faransa

2021-05-15 10:18:49
Firai Ministan Kasar Ivory Coast Ya Ce Ya Sami Lafiya Bayan Dawowarsa Daga Kasar Faransa

Patrick Achi firai ministan kasar Ivory Coast ya bayyana cewa ya sami lafiya bayan ya dawo gida Ivory Coast daga kasar Faransa inda yayi jinya na ‘yan kwanaki. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Patric Achi dan shekara 65 a duniya ya na fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda ya isa birnin Abidjan daga kasar Faransa.

A cikin watan Maris da ya gabata ne shugaba Alhasan Watara ya nada Achi a matsayin firai ministan kasar bayan mutuwar firai ministoci guda biyu a cikin watanni 8 a kasar.

Achi ya maye gurbin Mamed Bakayoka wanda ya rasu sanadiyyar cutar daji yana dan shekara 56 a duniya. Kafin haka Bakayoka ya maye gurbin Amadou Culebali ne wanda shi ma ya rusu a cikin watan yulin shekarar da ta gabata saboda rashin lafiya.

A makon da ya gabata ne Achi ya je kasar faransa don jinya, amma ya kuma halarci wani taro kan samar da makamaci a kasar ta Ivory coast a wannan tafiyar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!