Palasdinu:A Cikin Iyali Guda Yara 6 Ne Suka Yi Shahada A Zirin Gaza

2021-05-15 10:03:31
Palasdinu:A Cikin Iyali Guda Yara 6 Ne Suka Yi Shahada A Zirin Gaza

Yara 6 ne, a cikin iyali guda aka tabbatar da mutuwar a wani ruwan boma-bomai wanda jiragen yakin haramtacciyar kasar Isar’ila (HKI) suka yi a safiyar yau Asabar a yankin zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancinlabaran ‘Ma’an News’ na Falasdinawan ya habarta cewa banda yaran akalla wani mutum guda ya mutu a gidan, sannan wasu kimani 20 sun ji rauni a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-shati dake zirin na Gaza.

Fiye da mako guda kenan jiragen yakin HKI suke luguden wuta kan falasdinawa a zirin Gaza wanda ya zuwa yanzu mutane 133 ne suka yi shahada, 38 daga cikinsu yara kanana ne, sannan da mata 20. Banda haka wasu mutane 1000 sun ji rauni sanadiyyar hare-haren. MDD dai ta bada sanarwan cewa falasdinawa a zirin na Gaza kimani 10,000 ne suka bar gidajensu don kaucewa hare-haren na yahudawan Isra’ila ‘yan mamaya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!