Iraki: Muqtada Assadar Ya Kira Gagarumar Zanga-Zanga Ta Goyon Bayan Al-Ummar Falasdinu

2021-05-15 09:50:16
Iraki: Muqtada Assadar Ya Kira Gagarumar Zanga-Zanga Ta Goyon Bayan Al-Ummar Falasdinu

A dai-dai lokacinda kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai a yankin zirin Gaza suke ci gaba da cilla makaman roka a kan birnin Tel’abib babban birnin Haramtacciyar kasar Isar’ila, shugaban jam’iyyarsa siysa ta Sadar a kasar Iraki sayyeed Muqtadha Assadr ya bukaci Irakawa su fito zangar zangar yin allawadai da ta’asan da haramtacciyar kasar Isara’ila take aikatawa a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Sadr ya bukaci a kiyaye ka’idojin kiwon lafiya saboda hana yaduwar cutar korona a gangamin nay au Asabar, sannan ya dole ne a daga tukar kasar Falasdinu, sannan a kona tutocin Isra’ila da Amurka mai goyon bayanta.

A wani labarin kuma Khalid Mash’al shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas a wajen kasar Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa dole ne a kiyaye sharuddun tsagaita bude wuta tsakanin kungiyarsa da sojojin Isra’ila a duk wata tsagaita bude wuta da za’a yi nan gaba.

Khalid Mash’al ya kuma kara da cewa dole ne a dakatar da korar falasdinawa a unguwar sheikh Jarrah wanda ya haddasa rikici na baya-bayan nan. Sannan a cire duk shingaye masu hana Falasdinawa isa masallacin Al-Aqsa da kuma sakin duk Falasdinawan da aka kamma a baya-bayan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!