Iran:Persepolis FC 1-Esteghlal FC-0 A Gasar Cikin Gida

2021-05-15 09:14:05
Iran:Persepolis FC 1-Esteghlal FC-0 A Gasar Cikin Gida

Kungiyoyin kwallon kafa mafi girma a kasar Iran Pesepolis da Esteghlal sun yi wasa na karshe a cikin wasannin cikin gida a filin wasanni na Azadi dake nan Tehran a jiya jumma’a da misalign karfe 19.30 na yamma, inda aka tashi Persepolis ta ci kwallo guda Estighlal kuma ta na nema.

Wasan na jiya dai shi ne na mako na 23 kenan da fara wasannin kuma shi ne na karshe wanda da wannan nasarar kungiyar Persepolis ta zakara a gasar.

Dan wasan Persepolis Issa Alikasir ne ya saka kwallo tilo a wasan a ragar Estighlal, wanda kuma shi ne ya bawa kungiyarsa nasarar da ta samu a gasar a minta na 55 da farata.

Persepolis ta sami maki 45 da wannan nasarar wanda kuma ya maida ita zakara a wasannin gaba daya.Esteghlal ta rasa matsayi na 3 da maki 34, inda ta koma matsayi na 5 a gasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!