​Gamnatin Tarayyar Najeriya: Za A Fuskanci Matsaloli Matukar Dokar Biyan Albashi Ta Koma Hannun Jihohi

2021-05-03 20:58:20
​Gamnatin Tarayyar Najeriya: Za A Fuskanci Matsaloli Matukar Dokar Biyan Albashi Ta Koma Hannun Jihohi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa maida dokar karin albashi ta naira 30,000 mafi kankantar albashi daga Tarayya zuwa jihohi, ba za ta biya bukata ba.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, inda ya ce Dokar albashi Mafi Karanci dokar kasa ce ba ta jiha ba, saboda haka babu wanda yake da hurumoin komawa gefe shi kadai ya yi mata kwaskwarima.

Ana ci gaba da kai ruwa rana da wasu gwamnoni cewa ba za su iya biyan mafi karancin albashi na naira N30,000 ba, sai dai idan za su samu karin ninkin kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya.

Ministan kwadagon ya ce sabuwar dokar mafi karancin albashi ba abu ne da za a iya daukewa daga dokokin tarayya a maida na jihohi ba, kuma ba kundin doka ba ne da jihohi za su rika zabar dokar da ta yi musu su yi aiki da ita, wadda kuma ba ta yi musu ba, su ajiye ta, ya ce ba haka lamarin yake ba.

Tun da farko Shugaban Kungiyar NLC ta Kasa Ayuba Wabba, ya ce matukar aka yi gangancin daukar dokar mafi karancin albashi daga tarayya zuwa jiha, za a fuskanci matsaloli da bore a Najeriya.

Wabba ya ce mafi karancin albashi doka ce ta kariya da rage radadin talauci ga kananan ma’aikata.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!