​Hamas Ta Yi Kira Da A Hana Yahudawa Kutsa Kai Cikin Masallacin Aqsa

2021-05-03 20:51:31
​Hamas Ta Yi Kira Da A Hana Yahudawa Kutsa Kai Cikin Masallacin Aqsa

Kungiyar Hamas ta kirayi Falastinawa musamman mazauna birnin Quds da su hana yahudawa masu tsatsauran ra’ayi kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani wanda ta fitar a yau, Kungiyar Hamas ta kirayi Falastinawa musamman mazauna birnin Quds da sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan, da su bai wa masallacin Quds, dangane da shirin da yahudawa suke da shi na kutsa kai a cikin wannan masallaci mai alfarma, wanda suka shirya yi a ranar 28 ga watan Ramadan.

Bayanin ya ce a fili take cewa, yahudawan Isra’ila suna yin hakan ne domin tsokanar musulmi, ta hanyar keta alfarmar wurare masu daraja da alfarma na musulmi, wanda hakan ya hada da masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko.

Hamas ta ce Falastinawa za su kare kansu da dukkanin abin da ya sawaka daga cin zalun na Isra’ila, kamar yadda kuma ba za su zura ido yahudawa suna keta alfarar wuraren masu tsarki na addinin musulunci ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!