Habasha Ta Ayyana Kungiyar Kwatar ‘Yancin Tigray A Matsayin Ta ‘Yan Ta’adda

2021-05-03 13:55:49
Habasha Ta Ayyana Kungiyar Kwatar ‘Yancin Tigray A Matsayin Ta ‘Yan Ta’adda

Majalisar ministocin kasar Habasha ta amince da bukatar shelanta kungiyar ‘Tigray People Liberation Front (TPLF) da kungiyar Oromo Liberation Front (OLF-Shene) a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar.

Jaridar Egypt Daily da kasar Masar ta bayyana cewa majalisar ministocin ta dauki wannan mataki ne bayan da ta yi nazarin ayyukan wadannan kungiyoyi a kasar. Kafin haka dai kungiyar TPRF ta taba zama kawar gwamnatin tarayyar kasar n.

Amma bayan darewar Abiy Ahmed kan kujeral firai ministan kasar a shekara ta 2018 ya maida kungiyar saniyar ware, wanda ya tilastwa ministoci ‘ya’yan kungiyar wadanda suke aikin da gwamnatin kasar suka yi murabus.

Mutanen kibilar Tigray wadanda suke da mutane kimani miliyon 5, sun gudanar da zabubbukan lardi bayan da gwamnatin Abiy ta dage zabubbukama shekara ta 2020, amma gwamnatin ta ki amincewa da sakamakon zaben. Wannan ya sa gwamnatin Lardin Tigray ta dauki gwamnatin Abiya a matsayin gwamnati wacce bata da halarci. Wasu suna ganin wannan matakin da majal;isar ministocin ta dauka yana iya rufe kofar tattauna da kungiyar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!