Shugaban Kasar Nijar Muhammad Bazoum Ya Kira Yi Kasashe Da Su Yi Aiki Da Nauyin Da Ya Rataya A Wuyansu Dangane Da Kare Muhalli
2021-04-07 14:43:11

Shugaban
kasar ta Nijar wanda ya gabatar da jawabi ga kwamiti mai kula da muhalli da
kuma matsalar cutar corona ta hanyar bidiyo daga nesa ya kira yi kasashe da su
yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu a karkashin yarjejeniyar Paris ta kare
muhalli.
Shugaba Muhammad Bazoum a cikin
jawabin nasa ya bayyana cewa; Cutar Covid-19 da kuma kalubalen sauyin muhalli
sun zo a wani lokaci a tare, inda su ka ci dunun kasashen da suke fama da
matsaloli.
Shugaban kasar na jamhuriyar Nijar ya kuma ce: “ A nahiyar Afirka, ba ya ga fada da ake yi da cutar corona, da akwai kuma wata kokawar ta fuskantar sauyin yanayi.”
031
Tags:
shugaban kasar nijar
ya gabatar da jawabi
kwamiti mai kula da muhalli
yarjejeniyar paris ta kare muhalli
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!