Iran: Kungiyoyin Bada Agaji Na Hilal Ahmar Da Red Cross Na Iran Da Ivory Coast Za Su Karfafa Aiki Tare

2021-01-13 14:30:50
Iran: Kungiyoyin Bada Agaji Na Hilal Ahmar Da Red Cross Na Iran Da Ivory Coast Za Su Karfafa Aiki Tare

Shugaban kungiyar bada agajin gaggawa ta Hilal Ahmar ta Iran Karim Hatami ya gana da tokoransa na Red Cross Ivory Coast Mr Dal’us, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin aiki tare.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakato Hatami yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki kasar Ivory Coast.

Kafin haka dai kungiyar Hilal Ahmar ta kasar Iran ta gina babban asbiti a birnin Abidjan babban birnin kasuwanci na kasar Ivory Coast.

A nashi bangaren shugaban kungiyar Red Cross na kasar Ivory Coast ya godawa kasar Iran da gina wannan asbitin ya kuma kara da cewa kasashen biyu zasu yi aiki tare don horasda ma’aikatan kungiyar hanyoyin kubutar da rayokan mutane daban-daban wadanda kasashen biyu suka kore a kansu.


019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!