Falasdinu:Yahudawan Isra'ila Sun Kashe Wani Bafalasdine Tare Jikkata Wasu 5

2021-01-13 14:22:13
Falasdinu:Yahudawan Isra'ila Sun Kashe Wani Bafalasdine Tare Jikkata Wasu 5

Bafalasdine guda ya yi shahada a yayinsa wasu 5 suka ji rauni a lokacinda wata motar yaki na haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) wacce take sintiri a gabacin yankin yamma da kogin Jordan a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labaran Sama na kasar Falasdinu ya nakalto wani jami’an tsaro na Falasdinawa a yankin yana cewa da gangan, wata motar yakin ta HKI wacce take aikin sintiri a yankin Al-Ghawar ta buge wata mota dauke da ma’aika Falasdinawa a safiyar yau Laraba inda mutum guda ya yi shahada a yayinda wasu hudu suka ji rauni.

Labarin ya kara da cewa yahudawan basa son ganin Falasdinawa ma’aikata ko manoma a yankin, don haka da gangan suka yi haka don hanasu zuwa yankin.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!