Masar: Amurka Da Jumhuriyar Czech Sun Janye Daga Wasan Handball Na Kasa Da Kasa

2021-01-13 09:01:07
Masar: Amurka Da Jumhuriyar Czech Sun Janye Daga Wasan Handball Na Kasa Da Kasa

Kungiyoyin kwallon handball na kasashen Amurka da Jumhuriyar Czech sun fice daga kasar wasannin handballa ta kasa da kasa wanda za’a fara a yau Larana a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa, kasashen sun janye ne saboda bullar cutar Korona a cikin mafi yawan yan wasansu.

Labarin ya kara da cewa Amurka ce kasa ta biyu wacce ta janye daga gasar ya zuwa yanzu. Amma duk da haka ana saran kasar Masar mai masaukin baki zata bude wasan a tsakanin kungiyarta ta wasan Handbull da kasar Macedonia ta Arewa.

A halin yanzu dai kasar Switzeland ce zata maye gurbin Amurka a yayinda Macedonia ta Arewa a wasannin. Kasashe 32 ne zasu gudanar da gasar wasan Handaballa na kasa da kasa.

Wadanda suka shirya gasar sun kuduri anniyar kawo yan kallo 5000 a ko wace wasa, amma gwamnatin kasar Masar ta ki amincewa da hakan saboda yadda cutar Korona take yaduwa a kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!