Shahararren Dan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya, Diego Maradona, Ya Mutu

2020-11-26 08:53:51
Shahararren Dan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya, Diego Maradona, Ya Mutu

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniyan nan kuma dan kasar Argentina, Diego Maradona ya mutu sakamakon matsalar bugun zuciya da ya fuskanta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun dan wasan ya fitar a jiya Laraba, ya ce a jiya laraba din ne fitaccen dan wasan ya mutu bayan ya fuskanci matsalar bugun zuciya yana da shekaru 60 a duniya.

A shekarun 1980 ne dai tauraruwar Maradona din ta fara haskakawa a fagen wasan kwallon kafa musamman a shekarar 1986 lokacin da ya jagorancin kungiyar kwallon kafa ta kasarsa wato kasar Argentina wajen lashe kofin duniya na kwallon kafa da aka buga a kasar Mexico.

A kasar Argentina din dai shugaban kasar Alberto Fernandez ya sanar da makokin kwanaki 3 a daukacin kasar don jimamin mutuwar Maradonan wanda ake gani a matsayin wani gwarzo a kasar.

A farkon wannan wata ne dai aka yi masa tiyata don cire wani gudan jini da ya mamaye kwakwalwarsa.

‘Yan wasan kwallon kafa daban-daban ne dai suke ci gaba da fitar da sakonni nuna alnihin rashin wannan dan wasan wanda yana daga cikin sanannun ‘yan wasan da suka yi suna a duniya a fagen kwallon kafa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!