​Janar Salami : Yaki Da Iran Ya Fita Daga Cikin Zabin Makiyan Kasar

2020-11-25 21:45:22
​Janar Salami : Yaki Da Iran Ya Fita Daga Cikin Zabin Makiyan Kasar

Babban hafsan hafsoshin dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran (IRGC) Burgedia Janar Hussain Salami ya bayyana cewa yaki da kasar Iran ya fita daga cikin jerin zabin da makiyan kasar suke da shi, don fuskantarta.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta kasar Iran ta nakalto Salami yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake jawabi a taron hotunan bidiyo na zagayowan ranar kafa rundunar mayakan sakai ta Basij a nan Tehran.

Salami ya kara da cewa dakarun Basij sun taimaka sosai wajen kare kasar Iran daga makiyanta tun bayan kafata shekaru fiye da 40 da suka gabata, sannan suna taimakawa wajen ayyukan ci gaban kasa a bangarori da dama.

Har’ila yau a yau Burgedia Janar Husain Salami ya kaddamar da wasu shirye-shirye na kyautata ayyukan dakarun sa kai na Basij. A rana irin ta yau ce shekaru kimani 40 da suka gabata Imam Khomaini (q) wanda ya kafa Jumhuriyar Musulunci ta Iran ya bada umurnin kafa dakarun sakai na Basij na raunana a kasar. (19)

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!