An Tsawaita Halin Ko Ta Kwana A Kasar Tunisia Na Tsawon Wata Guda

2020-11-25 21:41:25
An Tsawaita Halin Ko Ta Kwana A Kasar Tunisia Na Tsawon Wata Guda

Ofishin fadar shugaban kasar Tunisia ta bada sanarwan cewa an tsawaita halin ko ta kwana a bangaren harkokin tsaron kasar na tsawon wata guda a duk fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto ofishin shugaba Qais Sa’id ya na bada wannan sanarwan a safiyar yau Laraba. Ya kuma kara da cewa wannan halin zai ci gaba har zuwa ranar 25 ga watan Dicemba mai zuwa.

Tun ranar 24 ga watan Nuwambar shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar ta Tunisia ta kafa dokar ta baci a duk fadin kasar bayan wani harin ta’addancin da aka kai a babban birnin kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma raunata mutane 30 da kuma raunata wasu.

Har’ila yau a wani harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wata motar bus dauke da sojoji masu gadin fadar shugaban kasa a birnin Tunis, a cikin ‘yan kwanakin ya kai ga mutuwar sojoji 12 da raunata wasu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!