​Iran Zata Fara Saida Makamanta Daga Gobe 18 Ga Watan Octoba

2020-10-17 10:47:17
​Iran Zata Fara Saida Makamanta Daga Gobe 18 Ga Watan Octoba

Kakakin jami’an diblomasiyyar kasar Iran a MDD ya bayyana cewa daga gobe Lahadi 18 ga watan Octoba kasar Iran zata fara saida makamanta ga kasashen duniyan da suke bukatarsu.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Ali Reza Miryusufi kakkain jami’an diblomasiyyar kasar Iran a MDD yana fadar haka a jiya jumma’a. Ya kuma kara da cewa. Majalisar da kuma kasashen duniya da dama basu amince da abinda Amurka take kira “takurawa mafi tsanani kan kasar Iran ba”.

Labrain ya kara da cewa bisa abinda kudurin kwamatin tsaro na MDD mai lamba 2231 ya kunsa daga gobe Lahadi an dagewa kasar Iran takunkuman saya da seyar da makamai na tsowon shekaru kimani 10.

Kakakin jami’an diblomasiyyar ya kammala da cewa kokarin Amurka ta kashe yarjejeniyar JCPOA ya tashi a banza.

Comments(0)