Nijar: An dakatar da komawa makarantu daga 1 ga watan Oktoba zuwa 15

2020-09-23 13:48:29
Nijar: An dakatar da komawa makarantu daga 1 ga watan Oktoba zuwa 15

Gwamnati ta dage lokacin komawa makarantu har sai zuwa 15 ga watan Oktoba, saboda yadda wadanda ambaliyar ruwan ta shafa suke zaune a cikin makarantun

Wannan bayanin ya zo ne a cikin wata sanarwa ta gwamnati wacce sakatarenta Zakaria Abdurahman ya sanya wa hannu a ranar 21 ga watan nan na Satumba.

A shekarar bana an yi mamakon ruwa, kamar da bakin kwarya, da hakan ya haddasa ambaliya a cikin yankuna da daman a jamhuriyar Nijar.

Bugu da kari ambaliyar ruwan saman ta haddasa asara ta rayuka da ta dukiya.


013

Comments(0)