Rasha Ta Ce Ba Ta Jin Tsoron Takunkuman Amurka Dangane Da Huldar Makamai Da Iran

2020-09-23 08:51:46
Rasha Ta Ce Ba Ta Jin Tsoron Takunkuman Amurka Dangane Da Huldar Makamai Da Iran

Gwamnatin kasar Russia ta bayyana cewa ba ta jin tsaron takunkuman tattalin arziki na kasar Amurka dangane da huldar makamai da kasar Iran .

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Ryabkov ya bayyana cewa barazanar Amurka ba ta za hana huldar Iran da Rasha Ba.

Daga karshe ya ce kasar Rasha ta saba da takunkman tattalin arziki na kasar Amurka.

A ranar 20 ga watan Tatumba da muke ciki ne dai Amurka ita kadai ta bada sanarwan cewa ta maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta durorawa Iran kafin yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2015.

Comments(0)