Gwamnatin kasar Ivory Coast Za Ta Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Watan Octoba Ko Da Jam’iyyun Adawa Sun Kauracea Masa

2020-09-23 08:43:47
Gwamnatin kasar Ivory Coast Za Ta Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Watan Octoba Ko Da Jam’iyyun Adawa Sun Kauracea Masa

Jam’iyya mai mulki a kasar Ivory Coasr ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Octoba mai zuwa ko da jam’iyyun adawa sun kauracewa a zaben.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Henry Konan Badie babban adawa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben na watan Octoba yana kira ga jam’iyyun siyasar kasar su kauracewa zaben na watan Octoba don nuna rashin amincewarsu ga tsayawa takara karo na ukku wanda shugaba Alhassan Watara yake yi.

Shugaban ya bayyana cewa an yi wa kundin tsarin mulkin koskorima wanda ya bashi damar sake tsayawa karo na biyu.

Ya zuwa yanzu dai mutane kinai 12 ne suka mutu tun lokacinda Watara ya bayyanananniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancij kasar yan makonnin da suka gabata kuma bayan rasuwar wanda ya zaba a ya gaje shi wato marigayi firai minister Colebaly

Header 1

Comments(0)