​Nigeriya: Magu Ya Bukaci A Rika Gudanar Da Bincike A Kansa A Sarari Ba Boye Ba Kuma A Ba Shi Damar Kare Kansa

2020-08-22 21:09:28
​Nigeriya: Magu Ya Bukaci A Rika Gudanar Da Bincike A Kansa A Sarari Ba Boye Ba Kuma A Ba Shi Damar Kare Kansa

Lauyan tsohon shugaban hukumar EFCC ya sake rubuta wa Shugaban Kwamitin Bincike, Ayo Salami cewa yana neman a yi wa wanda ya ke karewa adalci, ta hanyar ba shi kwafi-kwafi na zarge-zargen da ake yi masa a rubuce domin ya yi nazari.

Magu ya sake yin korafin cewa kwamitin yaki yi masa adalci, domin har yau ya hana shi takardun bayanan zarge-zargen da ake yi masa, ballantana ya yi nazarin su.

Sannan kuma ya yi korafin cewa bai san wainar da ake toyawa ba a zaman, in banda ya halarci duk wani zama da aka gayyace shi, ya ce ana ci gaba da gayyato mutane da dama, ciki har da wadanda EFCC ke bin diddigin harkallar da suka yi.

Magu ya kara da cewa akwai hakkin da ya rataya a kan Kwamitin Bincike, na ya rika ba shi kwafin zargin da ake yi masa, domin ta hanyar yin nazarin kan wadannan zarge-zargen, zai bi su daya bayan daya ya kare kansa a duk lokacin da aka ba shi damar yin hakan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin tun a ranar 6 Ga Yuli, kuma an ba shi wa’adin kwanaki 45 ya kammala binciken sa domin mika sakamakon ga Buhari, wanda ya kamata a kammala tun ranar 16 ga wannan wata na Agusta.

Tags:
Comments(0)