​Trump: Ina Hasashen Saudiyya Za Ta Kulla Alaka Da Isra’ila

2020-08-22 21:06:39
​Trump: Ina Hasashen Saudiyya Za Ta Kulla Alaka Da Isra’ila

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana da kyakkyawan zaton cewa Saudiyya za ta kulla alaka da gwamnatin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar Whute House ya bayyana cewa, yana imanin cewa, Saudiyya za ta kulla aalaka da gwamnatin Isra’ila a nan gaba.

Furucin na Trump ya zo ne bayan kalaman ministan harkokin wajen Saudiyya ya yi ne a ranar Laraba da ta gabata a kasar Jamus, inda ya ce UAE ta kulla alaka da Isra’ila ne bisa yarjejeniyar larabawa ta 2002, kuma Saudiyya za ta yi duk abin da yake karkashin wannan yarjejeniya, matukar zai kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Kasar UAE dai ta sanar da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a bayyane ne a makon da ya gabata, bayan kwashe tsawo lokaci ana gudanar da huldar a boye.

Tags:
Comments(0)