​Kenya: Gwamnati Ta Bude Babban Masallacin Nairobi

2020-08-22 20:59:03
​Kenya: Gwamnati Ta Bude Babban Masallacin Nairobi

Bayan kwashe tsawon watanni biyar bababn masallacin musulmin kasar Kenya yana rufe, gwamnati ta bayar da izini bude masallacin da ke birnin Nairobi fadar mulkin kasar ta Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na The Star cewa, an bude babban masallacin Juma’a na birnin Nairobi na kasar Kenya bayan kwashe tsawon watanni biyar yana rufe, sakamakon bullar cutar corona.

An bude masallacin ne bisa wasu sharudda na musamman na kiyaye kaidojin kiwon lafiya, daga ciki kuwa har da yin alwalla kafin zuwa masallaci, da kuma zuwa da darduma.

Haka nan kuma an kayyade adadin mutanen da za su iya yin salla a cikin masallacin wanda yake daukar masallata dubu 10 a lokaci guda, inda aka sanya dokar cewa mutanen da za su yi salla a ciki a lokaci guda kada adadinsu ya wuce dubu daya da 350.

Baya ga wannan kuma an saka sharadin cewa dole ne masallata su bayar da tazarar akalla mita 1.5, sannan kafi shiga cikin masallaci a wanke hannuwa, da kuma saka takunkumin fuska.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya bayyana cewa, za a iya bude wuraren ibada a kasar matukar za su kiyaye sharuddan kiwon lafiya da aka gindaya.

Tags:
Comments(0)