​Rundunar Kawancen Kasashen Yankin Tafkin Chadi Ta Rugurguza Sansanin ‘Yan Ta’adda

2020-08-22 20:53:37
​Rundunar Kawancen Kasashen Yankin Tafkin Chadi Ta Rugurguza Sansanin ‘Yan Ta’adda

Dakarun Kawancen kasashen yankin Tafkin Chadi sun rugurguza wani babban sansanin mayakan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi a yankin Tunbun Fulani a zirin tafkin Chadi.

Kakakin rundunar Kanar Timothy Antiga ya shaida cewa, dakarun MNJTF runduna ta uku sun auka wa mayakan ‘yan ta’adda ne daga bangaren Najeriya da manyan makamai.

Rahotanni dai sun tabbatar da sojojin rundunonin biyu sun yi wa ‘yan ta’adda barna sosai yayin wannan gumurzu.

Kanar Timothy Antiga ya ce kodayake kawo yanzu ba a tantance yawan barnar da aka yi wa kungiyar ‘yan ta’addan ba, to amma bayanan farko da aka tattaro ta hanyar na’urori ya nuna an yi wa masu ikirarin jihadin gagarumar barna.

Tags:
Comments(0)