Ana Ci Gaba Da Yin Tsokaci Akan Tsagaita Wutar Yaki A Kasar Libya

2020-08-22 14:10:39
Ana Ci Gaba Da Yin Tsokaci Akan Tsagaita Wutar Yaki A Kasar Libya

A jiya Juma’a ne dai shugaban majalisar wakilan kasar Libya Aqila Saleh ya kira yi dukkanin bangarorin da suke yaki da su tsagaita wuta.

Shi kuwa Fathi Bashaqaha wanda shi ne ministan harkokin cikin gidan kasar Libya, ya bayyana cewa; Ba domin taimakon Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiya da kuma Masar ba, to da ba a kai ga cimma tsagaita wutar yaki ba a Libya.

A wata hira da tashar talabijin din Bloomberg ta yi da shi, Bashaqaha ya kara da cewa; Abinda ya kamata ya biyo bayan tsagaita wutar shi ne tattauna wacce za ta kai ga samun kwanciyar hankali, kuma wajibi ne a dauki wadannan matakan da gaggawa.

Tun da fari, a jiya Juma’a ne shugaban kasar ta Libya Fayez Al-Sarraj, da kuma kakakin Majalisar wakilai Aquila Saleh su ka yi kira da a tsagaita wutar yaki, bayan tuntubar juna da aka yi akan rikicin kasar ta Libya.

Bugu da kari Al-Sarraj da Saleh sun yi kira da a dawo da hako man fetur da tace shi domin fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.

Tags:
Comments(0)