A Karon Farko Dan Hamayyar Siyasar Mali Da Aka Sace Ya Aiko Da Wasika Ga Iyalansa

2020-08-22 14:07:57
 A Karon Farko Dan Hamayyar Siyasar Mali Da Aka Sace Ya Aiko Da Wasika Ga Iyalansa

Sama’ila Cisse wanda masu ikirarin jihadi su ka sace a cikin watan Maris ana gab da gudanar da zabe, ya aike wa iyalansa wasiki wacce ita c eta farko a tsawon wannan lokacin.

Kungiyar agaji ta “Red Cross” ta sanar a jiya Juma’a cewa; Ita ce ta karbo wasikar ta Mr. Cisse ta mikawa iyalansa.

Cisse dan shekaru 70 shi ne jagoran jam’iyyar Union For the Republic Democracy ( URD) a takaice ya bace a ranar 25 ga watan Maris a yankin Timbuktu da ke tsakiyar Mali. A lokacin da aka sace shi yana yi wa jam’iyyarsa yakin neman zabe ne a zaben ‘yan majalisa da aka gudanar bayan sace shi da kwanaki hudu.

Babu cikakken bayani akan abinda wasikar ta kunsa, sai dai ta zo ne adaidai lokacin da kasar ta tsunduma cikin dambaruwar siyasa, bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Ibrahim bubakar Keita.

Tags:
Comments(0)