Isra'ila Ta Yi Wa Kungiyar Hamas Barazanar Kai Ma Ta Munanan Hare-hare

2020-08-22 14:04:27
Isra'ila Ta Yi Wa Kungiyar Hamas Barazanar Kai Ma Ta Munanan Hare-hare

Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta ce idan har makamai masu linzami su ka ci gaba da kai ma ta hare-hare to za ta mayar da martani mai tsanani.

Ministan yakin HKI Benny Gantz ne ya yi barazanar tsananta hare-hare akan cibiyoyin na kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas, idan har har aka ci gaba da tura balo-balo masu kuna daga Gaza zuwa sansanonin ‘yan share wuri zauna.

Mai Magana da yawun sojojin mamayar HKI ta ce; Sun kakkabo makamai masu linzami 12 da aka harba daga Gaza.

Su dau Palasdinawan Gaza suna mayar da martani ne akan hare-haren da ‘yan sahayoniya su ke kai musu da kuma killace su da aka yi tun a 2006.

A halin da ake ciki a yanzu, kasar Masar tana kokarin shiga tsakani domin hana barkewar yaki tsakanin ‘yan gwagwarmayar Gaza da kuma yahudawa ‘yan mamaya.

Sai dai majiyar Gaza ta ambato ‘yan gwgawarmayar na cewa ba za su mayar da wuka cikin kube ba sai idan ‘yan sahayoniyar sun dakatar da kai musu hari.

Dakin hadin gwiwa na tafiyar da yaki a Gaza wanda Hamas tana ciki, ya bayyana cewa; su ne ke da alhakin kai hare-haren mayar da martani a yankunan da suke karkashin mamaya.

Tags:
Comments(0)