Ministan Tsaron Kasar Iran Zai Kai Ziyara Kasar Rasha A Yau Asabar

2020-08-22 14:00:56
Ministan Tsaron Kasar Iran Zai Kai Ziyara Kasar Rasha A Yau Asabar

Ministan tsaron na Iran Janar Hatami zai ziyarci kasar Rasha a matsayin amsa gayyatar da takwaransa na kasar Sergey Shoygu ya yi masa.

Bugu da kari,ministan tsaron na Iran zai halarci taron baje-koli na soja karo shida kuma na kasa da kasa mai taken: “Army 20”

A kowace shekara ana yin baje kolin soja a kasar ta Rasha, inda kasar take nuna sabbin kere-keren da ta yi ta fuskar tsaro. Bugu da kari a wurin taron akan gabatar da tarukan da suka kunshi tattaunawar kwararru akan harkokin tsaro.

Iran tana da kyakyyawar alaka da kasar Rasha ta tattalin arziki da siyasa.

Har ila yau alakar kasashen biyu ta fuskar tsaro tana kara bunkasa.

Tags:
Comments(0)